Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta tabbatar da Hon. Salisu Yusuf Majigiri a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na kujerar majalisar wakilai da zai wakilci mazaɓar Mashi/Dutsi a zaɓen shekarar 2027.
An gudanar da taron tabbatarwar ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙaramar hukumar Mashi, ranar da jam’iyyar ta ware domin gudanar da zaɓukan fidda gwani a faɗin ƙasa.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyya daga matakin ƙasa da jiha, masu ruwa da tsaki, jami’an tsaro, wakilan hukumar zaɓe da kuma ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da suka hallara domin nuna goyon baya ga ɗan takarar.
Hon. Majigiri ya kasance ɗan takara guda ɗaya tilo da ya tsaya neman tikitin kujerar, ba tare da wani abokin hamayya ba, lamarin da ke nuna irin karɓuwa da amincewar da yake samu daga shugabannin jam’iyya da al’ummar mazaɓar Mashi da Dutsi.
Tabbatarwar ya biyo bayan sasanci da fahimtar juna da shugabannin APC da masu ruwa da tsaki suka gudanar domin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Da yake jawabi yayin taron, wakilin shugabancin APC na ƙasa ya yaba da yadda mambobin jam’iyyar suka nuna biyayya da haɗin kai ga tsarin sasanci, yana mai cewa hakan wata alama ce ta ƙarfin jam’iyyar a Jihar Katsina.
A nasa jawabin, Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya gode wa shugabannin jam’iyya da al’ummar Mashi/Dutsi bisa amincewa da goyon bayan da suka nuna masa, tare da alƙawarin wakiltar al’umma cikin gaskiya, adalci da kishin ci gaba idan Allah ya ba shi nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya kuma yaba da irin rawar da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ke takawa wajen bunƙasa jihar da kuma tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar APC a jihar.
Hon Majigiri shine ke riƙe da wannan kujera da yake so ya koma a karo na biyu.
