
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar bisa ikirarinsa na kwanan nan cewa Nijeriya a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta fi shiga tsanani akan zamanin mulkin soji, tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin abin da ke ƙoƙarin jirkita tarihi da ke cike da saɓani ga ainihin yadda al’amura suke.
Rahotanni sun bayyana cewa, Atiku ya yi furucin ne a lokacin da ya ke jawabi a taron siyasa da jam’iyyarsa ta ADC ta shirya, inda ya zargi gwamnatin na yanzu da tsananta wa al’umma a shugabancinta sama da na gwamnatocin mulkin soji.
Da yake tsokaci akan kalaman, Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Yaɗa Labarai, Sunday Dare a ranar Lahadi, ya yi tir da ikirarin Atikun inda ya ce hakan ya ci karo da haƙiƙanin abin da mulkin dimukraɗiyya ta ƙunsa.
A cewarsa, tsohon shugaban ƙasar ya samu damar furta irin waɗannan kalaman ne saboda ‘yanci da dimukraɗiyya ta bayar don haka babu adalci acikin hakan domin a halin da ake ciki gwamnatin na bai wa kowa damar yin hira da gidajen jarida, halartar tarukan siyasa da sukar ta ba tare da fargabar kamu ko gurfanarwa ba.
Sunday Dare ya bayyana cewa haɗa mulkin zaɓaɓɓen shugaba da na sojoji da ke cike da danniya da wahalar da ‘yan Nijeriya wajen tura su kurkuku, kashe su da korar su a wasu lokuta, ƙoƙari ne na sauaya asalin abin da ya faru a tarihance.
Ya kuma alaƙanta zancen tsohon mataimakin shugaban ƙasar da rashin nasara a takarar shugaban ƙasa a lokuta daban-daban da rashin gamsuwa da sahihancin harkokin dimukraɗiyya.
Kawo yanzu dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai fitar da wani sako na musamman ba akan martanin da fadar shugaban ƙasar ta yi masa akan al’amarin.
