Yan bindiga sun kashe ‘yan sandan kwantar da tarzoma uku a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Lamarin ya faru na a ƙauyen Guga da ke ƙaramar hukumar Bakori a lokacin da ‘yan sandan ke gudanar da sintiri a ƙauyen.

‘Yan bindigan ne suka buɗewa yan sandan wuta ba zato ba tsammani inda nan take suka kashe ‘yan sandan uku tare da raunana biyu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda na nan na bincike.

Kofur Usman Musa ya bada sunayen ‘yan sandan da aka kashe da yace akwai ASP Abubakar Abdullahi,Sifeto Umar Ahmed da Saje Kailani Kabir.

Sai waɗanda suka sami rauni da suka haɗa da kofur Daniel Japst da kofur Abdul’aziz Sani.

Ana zargin ‘yan bindigan sun gaba da bindigogi guda uku masu ɗauke da harsashi masu yawa.

By ukarofi