
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da batun damuwa da lafiyar Shugaba Bola Tinubu sakamakon wani ɗan tuntuɓe da ya yi a lokacin da ake tarbarsa a Birnin Ankara da ke ƙasar Turkiyya, ranar Talata, tana mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa Shugaban ƙasar na cikin ƙoshin lafiya kuma tuni ya fara gudanar da harkokinsa na ziyarar aikin yadda aka tsara.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana haka ta kafar X.
A cewarsa, tuni Shugaba Tinubu ya cigaba da gudanar da al’amuran da ya kai shi na tattaunawa da Shugaba Recep Erdoğan na ƙasar da wasu manyan jami’an gwamnati.
Ya ce, zaman da Tinubu zai halarta da jagororin ƙasar za su mayar da hankali ne akan ƙarfafa harkokin difulomasiyya tsakanin Nijeriya da Turkiyya ta yadda za a faɗaɗa haɗin-gwiwa a lamuran tsaro, kasuwanci da zuba jari, makamashi da kuma ci-gaban tattalin arziƙi.
Fadar Shugaban Ƙasar ta ƙara da cewa, cigaba da ziyarar abu ne da ke da tasiri ga ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu da kuma bunƙasa harkokinsu na dimukraɗiyya a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Da yake tsokaci akan tuntuɓen Shugaban Ƙasar, Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa al’amarin ba mai girma ba ne kamar yadda ake ta kururuta shi, saidai shugaban ya karci wani ƙarfe ne a ƙasa.
Wani gajeren bidiyo a kafar X ya janyo cece kuce inda aka hango shugaba Tinubu ya kusa faɗuwa suna tsakar tafiya da shugaba Erdogan.
