Kallon fina-finan Hausa na taimaka wa yawaitar kashe-kashe – Shugaban Izala na Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a cikin al’umma na da alaƙa da tasirin kallon wasu fina-finan Hausa da ke ɗauke da nuna tashin hankali, inji Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatissunnah (Izala) a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe.

Ya bayyana hakan ne yayin taron bitar da ƙungiyar Izala ta shirya wa malamai da limamai sama da 750 domin shirin tafsirin watan Ramadan na shekarar 2026 a faɗin jihar.
Salisu Gombe ya ce a wannan lokaci al’umma na buƙatar jagorancin malamai, saboda haka ya zama wajibi a shirya su yadda za su fuskanci jama’a a wuraren tafsiri da wa’azi domin gyara tarbiyya da kawo zaman lafiya.

“Idan aka bar malamai ba tare da tsari ba, jama’a za su shiga ruɗani. Amma idan aka musu bita aka ja hankalinsu, al’umma za ta samu nutsuwa,” inji shi.

Ya ƙara da cewa shan miyagun ƙwayoyi na lalata tunanin matasa, sannan kallon fina-finai da ke nuna yadda ake kashe mutane na ƙara sa wasu ɗaukar tashin hankali a matsayin abin koyi.
“Yaro ko matashi idan kullum yana kallon fina-finai masu nuna faɗa, bindiga da kisan kai, zai ɗauki hakan kamar wasa. Miyagun ƙwayoyi kuma sukan ƙara ruguza masa hankali,” inji Salisu.

Ya bayyana cewa a Gombe an taba samun wani yaron shago da ya caka wa maigidansa almakashi har ya kashe shi saboda saɓani, abin da ke nuna yadda gurɓatar tunani ke jawo laifi.

Shugaban Izalan ya buƙaci gwamnati da hukumomi su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi, tare da sanya ido kan abubuwan da ake nunawa a fina-finan Hausa domin kare yara da matasa.

Ya ce malamai kuma suna da rawar da za su taka wajen wayar da kan jama’a a kan illar tashin hankali, shaye-shaye da kwaikwayon abin da ake gani a talabijin da wayoyi.

Salisu Gombe ya kuma ja hankali kan wasu da ke kiran kansu ‘yan Alƙur’ani zalla, yana mai cewa idan ba a shirya malamai yadda ya kamata ba wajen fahimtar da jama’a matsayinsu, hakan na iya haddasa rikici a cikin al’umma.

A ɓangarensa, Dakta Kabir Bashir Abdulhamid daga Jihar Kano ya gabatar da maƙala kan irin waɗannan aƙidu, yana mai cewa suna haddasa ruɗani a tsakanin Musulmi.
“Bin koyarwar shari’a da tsarin da aka gada ne zai kare al’umma daga faɗawa koyarwar da ba su da tushe,” inji Dakta Kabir.

Shugaban kwamitin shirya taron, Farfesa Rasheed Abduganiy, ya bayyana cewa bitar na taimaka wa malamai su bi ƙa’idojin da suka dace wajen koyarwa da tafsiri.
Ya ce ƙaruwar mahalarta daga bara zuwa bana na nuna yadda malamai ke fahimtar muhimmancin gyaran tarbiyya da zaman lafiya a cikin al’umma.

By ukarofi