Ƙungiyar tsangaya ta samar wa malaman tsangaya cigaba a ƙasa

Spread the love

Ƙungiyar Tsangaya ta samar wa malaman tsangaya cigaba a ƙasa tare da Gwani Ibrahim Mai Bindiga Hadejia .

Taron da aka gudanar da shi yau Talata 27 ga watan Janairu a ɗakin taron na Naicon Luxury Hotel dake Abuja ya samu halarta manya Shaihunnai da gwanenyen Al’qurani mai girma daga sassan daban-daban na faɗin kasar nan.

Manya gwanayen da shaihunnai Al’qurani mai girma sun bayyana taron a matsayin wani babban cigaba a ƙungiyar tsangaya wanda naɗa Gwani Ibrahim Mai Bindiga zai samarwa Almajirai damar-maki a matakai daban-daban.

Haka kuma gwanayen sun bayyana cewa ƙungiyar Tsangaya kullum burinta shine fafutikar nemawa Almajirai ‘yanci da ababen yi tare da shigar da buƙatunsu a gurin gwamnatocin ƙasa.

Da yake nasa jawabin sabon shugaban ƙungiyar tsangaya Gwani Ibrahim Mai Bindiga ya gode wa Allah bisa wannanan dama da ya bashi inda ya bayyana cewa za suyi aiki tuƙuru wajen samar da cigaba a Almajirai a duk faɗin ƙasar nan.

Haka kuma Gwani Ibrahim ya buƙaci cikekken goyon baya daga membobin ƙungiyar ta tsangaya domin a gudu tare a tsira tare.

Naɗin na Gwani Ibrahim Mai Bindiga na zuwa ne duba da ƙoƙarin sa a matsayin Shugaban Tsangaya na Jihar Jigawa wanda ya shafe shekaru tara kan kujerar. Inda ya samar da gagarumin cigaba.

By ukarofi