Alhaji MK Ahmed ya kwanta dama

Daga WAKILINMU

Allah Ya yi wa Sarkin Yaƙin Lokoja, Alhaji MK Ahmed (MFR), rasuwa.

Marigayin wanda tsohon sakatare ne ga marigayi Malam Aminu Kano, ya rasu ne da safiyar Asabar bayan fama da rashin lafiya.

Jaridar Prime Time ta rawaito cewa, marigayin ya bar duniya yana da shekara 89.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama, ciki har da Barista Naseer Ahmed, mamallakin fitaccen Otale ɗin Grand Central da ke Kano.