Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce ba yin Allah ba ne Nijeriya ta yi fama da matsalar tattalin arziki, yana mai cewa kasar na da albarkatu masu yawa.
Tsohon shugaban na Nijeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 40 na Archdiocese na Abuja a Abuja a ranar Lahadi, 13 ga Oktoba.
Obasanjo ya jaddada cewa Nijeriya na da duk abin da take bukata don ci gaba.
“Kamar yadda Allah ya halicci sauran al’ummai, ya ba su albarkatu, haka nan kuma ya albarkaci Nijeriya da albarkatu masu yawa don ci gaba. Kamar yadda kasar Masar ke da kogin Nilu, Nijeriya na da kogunan Neja da Benue, da kuma ɗanyen mai, da kasa mai albarka, da sauran albarkatun kasa. Na yi imani Allah bai halicci Nijeriya don gwagwarmaya ba. Ya ba mu duk abin da muke bukata; hakkinmu ne mu gode masa, musamman ganin cewa kasashe da dama ba su da abin da Nijeriya ke da shi.”
Obasanjo ya bukaci shugabanni, malamai da ’yan kasa da su yi wa kasar addu’a domin samun lafiya, tare da sanin cewa halin da Nijeriya ke ciki ba laifin Allah ba ne.
“Mun ɓarnata baiwar da Allah ya ba mu, amma idan muka kasɗantar da kanmu muka neme shi, zai warkar da kasarmu,” ya ce
