‘Yan siyasa ne ke haifar da ƙaruwar shaye-shaye ga matasa – Kawu Sumaila

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kawu Sumaila, Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, ya ce wasu ‘yan siyasa da bai fadi sunayensu ba na haddasa yawaitar amfani da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sumaila ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a zauren majalisar dattawa, yayin da ya ke ba da gudunmuwa a muhawara kan ƙudirin dokar da ke neman kafa cibiyar ƙasa ta wayar da kan jama’a game da amfani da ƙwayoyi da kuma gyaran hali.

Sanata Rufai Hanga wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya, shi ne ya gabatar da ƙudirin.

Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu ya bayyana cewa wasu daga cikin gidajen ‘yan majalisa da ofisoshin mazaɓu ana amfani da su wajen ɓoye ƙwayoyi ta hannun ma’aikatansu.

Shugaban kwamitin wasanni ya ce ya zama dole a riƙa tilasta wa ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati yin gwajin ƙwayoyi kafin a gudanar da zaɓe ko naɗa su muƙami.

“Dole mu samar da yanayin da kafin a gudanar da zaɓe ko naɗa muƙami, sai an yi gwajin ƙwayoyi,” inji shi.

“Yayin da nake magana yanzu, yawancin jami’anmu a mazaɓunmu, yawancin jami’an siyasa, yawancin gidajenmu, idan ka shiga, za ka ga tarin ƙwayoyi a can.”

By ukarofi