Ranar Abinci Ta Duniya: Monoma  matan Zamfara sun yi bajekolin kayan noma

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Kungiyar Mata Manoma ‘Nigerian Association of women in Agriculture’ (NAWIA), reshen Jihar Zamfara tare da haɗin gwiwa da ofishin matar gwamnan jihar, Hajiya Huriyya Dauda, sun gudanar da bikin Ranar Abinci ta Duniya, inda suka bajekolin hajarsu na amfani gona da kowacce ƙaramar hukuma ke nomawa a ranar Laraba da ta gabata. 

A jawabin ta uwar gidan gwamna, Dauda Lawal, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana cewa, Majalisar ɗinkin Duniya ta ayyana ranar Abinci ta Duniya tana mai jaddada cewa, matan Jihar Zamfara ba a bar su a baya ba wajen nuna ma duniya amfanin gonan da suke nomawa, don dogaro da kai da cigaban tattakin arzikin jihar da ma ƙasa bakiɗaya.

“A yau mata manoma mun fito daga cikin ƙanana hukumomi 14, don nuna wa duniya noman da muke yi da kuma yadda za a sarafa shi ya zuwa abinci. Don haka insha Allah a shekara mai zuwa mata manonan Jihar Zamfara za su bayar da mamaki wajen ƙara ƙaimi na gabatar da amfanin gona da mu ke nomawa da hannunmu,” inji ta.

Hakazalika, Huriyya Dauda ta jinjina wa ƙungiyar NAWIA a ƙarƙashin jagorancin Shemau Lado akan zamowarta kallabi tsakanin rawuna a sashen noma.

Babban baƙo mai jawabi kuma Kwamishin ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Zamfara, Hon. Ahmad Yandi, ya bayyana cewa, ƙudirin Gwamnatin Jihar Zamfara shine bunƙasa noma.

Ya ƙara da cewar, gwamnatin jihar ta raba takin zamani da iri kyauta ga manoman Zamfara, don bunƙasa tattakin arzikin jihar. 

A nata jawabin, shugabar ƙungiyar, Hajiya Shemau Lado, ta bayyana cewa, ranar manoman ta duniya a matsayin rana mai matuƙar mahimmanci, tana mai cewar, mata manoman a jihar sun samu nasara a daminar bana matuƙa. 

“Wannan nasara mun same ta ne tare da goyan bayan uwar gidan Gwamna Dauda, Hajiya Huriyya, da ta ke ba mu a koda yaushe da kuma ƙarfafa mu akan dabarun cigaban noma na zamani.

By ukarofi