Waɗanda suka kashe Hanifa a Kano sun nemi kotu ta soke hukuncin kisa a kan su

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu mutum biyu da aka samu da laifin yin garkuwa da kisan Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar, Abdulmalik Muhammad Tanko da Hashimu Isyaku, sun shigar da kara kotu inda suke ɗalubalantar hukuncin kisa a kotun ɗaukaka ɗara da ke Kano.

Idan za a iya tunawa, a ranar 28 ga watan Yuli, 2022, wata babbar kotun jihar Kano ɗarɗashin jagorancin mai shari’a Usman Mallam Na’abba ta yanke wa mutanen biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan shari’ar.

Sannan kuma an yanke musu hukuncin shekaru biyar da huɗu kowannensu bisa laifin haɗa baki, domin dukkansu sun haɗa baki tare da yin garkuwa da marigayiyar daga gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Islamic Foundation, tare da kashe ta tare da binne ta a wani ɗan ɗaramin kabari a makarantar share fage na Arewa maso Yamma da ke Kwanar ‘Yan Ghana a ɗaramar Hukumar  Nassarawa, Kano.

Waɗanda suka shigar da ɗara ta bakin lauyansu Barista Anthony Ezenwoko, sun garzaya kotun ɗaukaka ɗara da wasu dalilai guda biyu na ɗaukaka ɗarar, inda suka buɗaci kotun ta yi watsi da hukuncin kisa da aka yanke musu.

Abdulmalik da Hashimu sun yi zargin cewa hukuncin da kotun ta yanke bai dace ba kuma ba za a iya goyan bayan shaidun da aka gabatar a gaban kotun ba.

Sun kuma yi zargin cewa alɗalin kotun ya yi kuskure a shari’a lokacin da ya ce mai gabatar da ɗara ya tabbatar da ɗarar ba tare da wata shakka ba.

Kwamitin shari’a na mutum uku, ɗarɗashin jagorancin mai shari’a B.M. Ugo, tare da Justice U.A. Musale da Justice A.O. Adeniyi, ya amince da buɗatar lauyoyin masu ɗara na ɗara tsawaita ɗaukaka ɗara, yana ɗalubalantar hukuncin babbar kotun jihar Kano mai lamba biyar a ɗara mai lamba K/30e/2022.

Lauyan waɗanda suka shigar da ɗaran ya nemi a ranar 12 ga Agusta, 2024, inda suka buɗaci a ɗara musu lokaci domin ɗalubalantar hukuncin kisa da babbar kotun jihar Kano ta yanke. Lauyan gwamnatin jihar Kano bai yi watsi da wannan buɗata ba.

Mai shari’a Ugo ya baiwa masu ɗaran damar ɗara tsawaita ɗaukaka kara a cikin kwanaki 14 a babbar kotun jihar Kano, musamman dangane da sanarwar ɗaukaka ɗara.

Ya ci gaba da cewa hukunce-hukuncen sun yi daidai da dokar kotun ɗaukaka ɗara, wacce ta ba da damar tsawaita lokaci a wasu yanayi.

By ukarofi