Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta sauya sunayen tituna da duk wasu abubuwa da ke ɗauke da sunayen Faransa, a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na yanke duk wata hulɗa tsakaninta da tsohuwar gijiyarta.
Mai magana da yawun gwamnatin sojin Col Maj Abdurrahman Amadu ne ya sanar da hakan, tare da kare matakin da cewa ya zama wajibi domin maye gurbin sunayen da gwarazan jamhuriyar ta Nijar.
Manjo Abdurrahman Amadu ya ce yawancin sunayen da aka sanya wa manyan titunan birnin Yamai, babu abin da suke tunawa ‘yanƙasar face baƙar wuyar da suka sha da uƙuba a lokacin mulkin mallaka da Faransa ta yi wa ƙasar.
An sauya titin nan da ke ɗauke da sunan janar Charles de Gaulle na Faransa, tare da maye gurbinsa da sunan fitaccen ɗan siyasar nan na Nijar Djibo Bakary, wanda ya taka muhimmiyar rawa a lokacin kokawar karɓar ‘yancin kai.
Sai kuma Place de la Francophonie da ya koma Place de l’Alliance des États du Sahel (AES)”, domin tunawa da haɗin kan ƙasashen yankin sahel da jamhuriyar Nijar ta ƙulla da maƙwabtanta wato Mali da Burkina Faso domin ƙarfafa tsaro da siyasar ƙasashen.
Kungiyar ƙasashen yankin Sahel ta La Francophonie ta dakatar da su daga cikinta tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasashen suka yi wa gwamnatocin farar hula.
A wani mataki na yauƙaƙa dangantaka tsakanin Nijar da makwabtanta, gwamnati ta maye gurbin mutum-mutumin kwamandan Faransa Parfait-Louis Monteil, da na fitaccen ɗan gwagwarmayar nan na Afirka kuma shugaban Burkina Faso da aka kashe Thomas Sankara.
Kawo yanzu ba a san martanin da Faransa za ta mayar kan hakan ba, sai dai abin ba zai zo da mamaki ba ganin cewa ba wannan ne karon farko da sojojin yankin Sahel ke ɗaukar mataki irin wannan a kan tsohuwar gijiyar ta su ba.
Tun bayan hamɓarar da mulkin shugaba Muhammad Bazoum a shekarar da ta gabata, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke duk wata hulɗa da Faransa da sauran ƙasashen yammacin duniya.
Sun kuma haɗa kai da ƙasashen Mali da Burkina Faso wajen kafa ta su ƙungiyar, da gayyato Rasha domin taimaka mata a fannin soji, don yaƙi da masu ta da ƙayar baya da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Duk da taimakon da Rashar ke bai wa yankin, har yanzu ƙasashen uku na fama da matsalar masu iƙirarin jihadin.
