Sabbin tsare-tsaren Sa’adatu Liman yana inganta ilimi a Jami’ar Jihar Nasarawa, inji Akaro Mainoma

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An yaba wa Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Liman dangane da tabbatar da daurewar al’adun jami’ar  tun da ta hau ragamar mulkin kawo yanzu.

Tsohon Shugaban Jami’ar Farfesa Mohammed Akaro Mainoma ne ya bayyana haka a jawabinsa a wajen wani taron gabatar da lacca na musamman wato Inaugural lecture a Turance wadda jami’ar ke yi a wata-wata da aka gudanar a babban ɗakin taron jami’ar a mako da ake ciki.

Farfesa Mohammed Akaro Mainoma ya ce dole a yaba wa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman idan aka yi la’akari da yadda kawo yanzu a cikin ƙalilan watanni da ta yi a kujerar jagorancin jami’ar ba kawai tana tabbatar da cigaba daga inda tsofaffin shugabannin suka tsaya a fannin ayyukan cigaba kaɗai ba amma tana ma zarce waɗanda aka gudanar a baya ta sabbin kyawawan shirye-shirye da tsare-tsarenta.

Ya bada misali da yadda a cikin kwanaki 100 kacal da shugabar jami’ar na yanzu Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yi ta tallafa aka iya gudanar da ire-iren lacca-lacca ɗin na musamman da dama fiye da waɗanda aka gudanar a lokutan tsofaffin shugabannin da sauran ayyukan na cigaba a fannoni dabandaban a makarantan.

Daga nan sai tsohon shugaban Farfesa Mohammed Akaro Mainoma ya buƙaci Farfesa Sa’adatu ta cigaba da hakan inda ya tabbatar mata cewa anasu bangaren zasu cigaba da bata cikakken goyon baya sa’anan ya kuma bukaci sauran shugabanni da ma’aikatan babbar jami’ar ta gwamnatin jihar baki daya a duka matakai suyi koyi da Sa’adatu Hassan Liman su kuma cigaba da bata goyon bayo don ta samu damar cigaba da inganta harkokin ilimi a jami’ar.

Ita ma da take jawabi a wajen taron shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yaba wa wanda ya gabatar da laccar na wannan watan wato Farfesa Abdullahi Adamu Suleiman dangane da gudumawa da ya dade yana bayar a fannin Ilimi a jami’ar musamman ilimin addinin Islamiya inda ya kware inda ta kuma bayyana cewa tabbas idan shugabanni a duka matakai musamman ‘yan siyasa a ƙasar nan zasu yi aiki da darusa dake cikin laccar tabbas da za a iya magance wasu matsaloli da cin hanci da rashawa da talauci da sauran su da al’umma ke fuskanta a yanzu.

Ta ce baya ga amfani da laccar zai yi wa ƙasa baki daya zai kuma je nesa ba kusa ba wajen jawo hankulan musamman al’ummar musulmi wajen tsoron Allah a zukatan su ayayin da suke gudanar da harkokin su na yau da kullum inda ta bukaci kowa ya tabbatar yayi aiki da darusan.

A nasa ɓangaren day ake gabatar da laccar Farfesa Abdullahi Adamu Suleiman ya bayyana wasu ire-iren banbanci ne da ake samu tsakanin yanayin shugabanci na zamani dana addinin musulunci inda yayi kira ga shugabanni a duka matakai a ƙasar nan su rika saka tsoron Allah a zukatan su don a samu al’umma tagari

By ukarofi