Almundahana: Saraki ya shiga hannun EFCC

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zangon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) ta cafke tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, kan zargin sata da almundahanar dukiyar gwamnati, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Saraki wanda tsohon gwamna ne a Jihar Kwara, ya faɗa a komar EFCC ne ran Asabar da ta gabata, lamarin da wasu ke ganin cewa hakan ka iya zama mafarin wani sabon ƙalubale ga ɗan siyasar.

A matsayinsa na shugaban Majalisar Dattawa tsakanin 2015 da 2019, Saraki ya fuskanci zarge-zarge na rashawa da shararaa da bayanan ƙarya game da kadarorin da ya mallaka wanda Kotun Ƙoli ta wanke shi a Yulin 2018.

Sai dai a wannan karon, jaridar Premium Times ta fahimci cewa EFCC ta buƙaci Saraki ya amsa mata tambayoyi ne kan abin da ya shafi zargin yin amfani da wasu kamfanoni wajen satar kuɗaɗen gwamnati.

An yi zargin cewa kamfanonin da aka yi amfani da su wajen aiwatar da kwangiloli ga jihar Kwara ƙarƙashin Saraki, sun tara wa Sarakin kuɗaɗen haramun na shekaru da dama.

Sahihan bayanai sun nuna an yi amfani da waɗannan kamfanoni wajen tara ɗaruruwan milyoyi na Naira a lokuta daban-daban.

Haka nan, jami’an EFCC sun mallaki jerin sunayen kamfanonin da lamarin ya shafa inda suka bincika haramtattun hada-hadar da aka gudanar tsakaninsu da Saraki.

Bayanan da Premium Times ta kalato sun nuna cewa, ɗaya daga cikin kamfanonin shi ne ya ɗauki nauyin ɗawainiyar rayuwar Saraki, da ya haɗa da biya masa kuɗin hayar gidansa da ke Maitama da yi masa kwaskwarima inda ake kashe ɗaruruwan milyoyi na Naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *