“An bar Arewa a baya ta fuskar samun damar karatu kyauta”
Daga ABUBAKAR M. Taheer
Dakta Habiba Iliyasu Atta wadda senior lakcara ce a Department ɗin Microbiology na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A cikin wannan tattaunawa da wakilinmu Abubakar M Taheer ya yi da ita, ta kawo matsalolin dake saka ƴan Arewa rasa damar samun guraben karatu a ƙasashen waje. Haka kuma Dakta ta kawo irin nasarorin da ta samu wajen samun ‘scholarship’ na PTDF da hanyoyin da mutum zai bi wajen samun irin damar da ta samu, wato ‘scholarship’ ɗin, tare kuma da bayyana mana irin ƙalubalai da ke kan matasan ƙasar nan kan ilimi wanda ƙasashen duniya suka cigaba ta ɓangarensa. A sha karatu Lafiya.
MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu.
DAKTA HABIBA: Assalamu alaikum warahamullah. Sunana Dakta Habiba Iliyasu Atta, wanda malama ce a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na shafe kusan shekaru 17 a jami’ar Ina aiki. Na yi digiri na na farko da na biyu, har ma da na uku, wato PHD duk a jami’ar ta ABU inda bayan kammala ‘masters’ na samu aiki da jami’ar.
Za mu so mu ji qarin bayani game da damar yin karatu kyau, wato ‘scholarship’ da PTDF ta ke bayarwa.
To, shi ‘scholarship’ ɗin PTDF an buɗe shi ne domin bada tallafin karatu ga ƴan Nijeriya ganin tana cikin ƙasashen da ke da albarkatun man fetur.
Wannan tasa ake ƙarfafa wa dukkan wanda yake karantar ɓangaren Injiniyanci da vangarorin kimiyya da ma ɓangaren ‘management’ dukkan su sukan amfana da wannan damar.
Akan bada damar ne tun daga kan digiri na ɗaya, ”masters” da PHD dama ɗaliban da ke a gida akan tallafa musu da kufi domin cigaba da karatunsu.
Wannan damar ba wai ta ƴan kudancin qasar nan bace, ta duk ƴan Nijeriya ce. Ina nufin babu bambanci ɗan Arewa ko ɗan Kudu, sukan bada damar ne ga wanda suka kammala digiri da First Class ko 2.1 wanda suke son samun damar tafiya ”masters” kenan.
Haka kuma akan gudanar da jarrabawa a da, yanzu akan cike ne a ‘Portal’ ɗinsu, sannan za su gayyaci mutum zuwa ‘interview’.
Yawanci wanda suke gudanar da ‘interview’ ɗin farfesoshi ne sukan gudanar da ita za ma su duba takar sakandiren mutum.
Misali, wanda ya nemi ɓangaren ‘Chemical Engineering’, za su duba shin mutum ya ci Chemistry lokacin yana sakandire, idan bai ci ba, gaskiya babu yiyuwar zai samu.
Haka kuma wanda ya nemi ”masters” zai rubuta bayani na ƙashin kansa wanda yake nuna buƙatar sa ga samun damar yin wannan karatun.
Su masu gudanar da ‘interview’ ɗin sukan duba wannan ‘Proposal’ ɗin sosai wanda yawanci za ka ga mutane da yawa basa rubuta wa da kyau wanda hakan yakan hana mutum samu.
Wani lokaci za ka ga ƴan Kudu suna muhimmantar da samun wannan damar, daga yaro ya kammala digirinsa da kyakkyawan sakamako zakaga ya nemi wanda ya samu irin wannan damar ya nuna masa hanyoyin da zai bi wajen samun.
Wannan tasa za ka ga kusan duk shekara su ne suke samun sama damu. Duk da su masu bada wannan damar sukan yi ƙoƙarinsu wajen ɗaukan dukkan wanda suka fito daga ɓangarorin ƙasar nan.
Abin takaici za ka ga wani lokacin wasu mutanen sukan taso daga kudanci ƙasar nan, sun yi amfani da damar wajen samun tunda mu ba a shirye muke su masu ba.
Haka kuma za ka ga kusan mu anan Arewa an bar mu a baya sosai a ɓangaren samun dukkan damar maki a duniya ma gabaɗaya.
Waɗanne nasarori za a ce kin samu ta sanadiyyar samun wannan dama ta karatu?
To Alhamdulillah, kusan zan ce dama ni tun tasowa Ina da burin yin karatu tun Ina ƙarama na taso gidanmu ana da ƙarfafa mutum ya yi karatu. Wannan tasa bayan na kammala digirin farko na cigaba da digiri na biyu inda na samu damar samun aiki a jami’ar ABU.
Bayan na gama ‘masters’ na fara gwada sa’a ta har sau biyu a PTDF amma ban samu ba. Wannan tasa na kara ƙaimi wajen Neman wani ‘scholarship’ ɗin duk na PTDF ce inda za ka je waje kayi wata shiga a UK, daga nan ka dawo Nijeriya domin ci gaba da karatu anan za ka kammala PHD ɗin dama kuɗin yin ‘research’ ɗin. Inaga 2010 na samu damar na kuma tafi 2013.
Bayan nan na sake komawa UK wajen ci gaba, a 2015 domin ƙarasa aiki na kuma samu nasara kammala PHD a 2016. Na kuma ci gaba da bincike domin samun damar sanin abubuwan da yawa. Saboda ɗalibai na su amfana haka na sake samun wata damar a US, domin ci gaba da karatun. Gaskiya Alhamdulillah.
Wane ƙalubalai ne ki ke ganin yake hana ƴan Arewa samun Irin wannan damar?
To a gaskiya na farko rashin wanda zai nusar da kai yadda zaka samu kusan shi ne abu na farko da ke damun mu.
Duk da mutanenmu sun fara farkawa yanzu ana ƙoƙarin wayar da kan hanyoyin da za a samu damar. Haka kuma abu na biyu shi ne, rashin haƙuri mutanenmu suna da gaggawar sai sun samu abu cikin ƙanƙanin lokaci. Misali ni a ƙashin kaina na cike har sau biyu sai a na ƙarshe na samu wannan damar.
Dole mutum ya yi haƙuri ya rinƙa gwadawa, ya rinƙa nema lokaci bayan lokaci idan har Allah Ya sa mutum yana da rabo, zai samu.
Sannan dukkan abinda ake da buƙata ka cike ka yi ƙoƙari ka rubuta shi daidai kamar ka ɗauki ‘Proposal’ na ‘masters’ ko PHD mutum ya yi ƙoƙari wajen nuna muhimmanci ilimi gare shi da damar da yake da ita wajen taimaka wa al’ummar sa wajen ilimi domin gaba.
A ƙarshe wane kira ki ke da shi ga iyaye mata wajen ba wa ƴaƴansu mata damar karatu?
A gaskiya na gode wa wannan tambaya, ya kamata iyaye su rinqa ba ma yaransu musamman mata dama su rinƙa samun damar yin karatu mai zurfi, wannan yake nuna duk yarinyar da ta samu karatu za ka ga al’umma sun amfan da ita sama da maza.
Za ta zama uwa wanda za ta koyar da yaranta. Yara mata dayawa za ka ga suna da bai wa, amma rashin samun ƙwarin gwiwa kan saka su su rasa wannan damar. Ba an ce kar a yima yarinya aure ba, a’a. Ya zama yarinya idan an tabbatar akwai son karatu a tare da ita a ba ta wajen cimma burinta na rayuwa.
Mun gode.
Na gode ƙwarai.