Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Alwan Hassan, ya nemi afuwar shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin kan zargin da ya yi musu na karɓar cin hancin dala miliyan goma domin hana tabbatar da Ramat Abdullahi a matsayin Shugaban hukumar kula da lantarki ta ƙasa NERC.
Hassan ya amince cewa zargin da ya yi musu da sauran jagorancin majalisar dattawa ba gaskiya ba ne, kuma ba adalci ba ne ga majalisar da shugabanninta.
A wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a wannan Talata, Hassan ya nemi cikakkiyar gafara, inda ya ce abin da ya furta a baya sakamakon bayanan da ya samu ne a baya ba tare da tabbatarwa ba.
Kazalika, ya bayyana cewa daga baya ya gano cewa babu wata hujja ko tushe da ke goyon bayan zargin da ya yi, don haka ya janye maganarsa tare da neman afuwa daga shugabannin majalisar dattawan Najeriya.
Zargin na manyan shugabannin na majalisa dai ya jawo zazzafar suka ga Alwan Hassan musamman daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau waɗanda suka sha alwashin maka shi a gaban kotu.
