‘Yan matan Kebbi: Shugaban sojoji ya kai ziyara, ya umarci dakarun tsaro su gaggauta ceto su

Spread the love

Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun rundunar ‘Operation Fansan Yamma’ da su ƙara himma wajen ganin sun ceto ɗaliban da aka sace a ‘Government Girls Comprehensive Senior Secondary School (GGCSS), Maga’, da ke karamar hukumar Danko-Wasagu ta Jihar Kebbi.

Janar Shaibu ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin wata ziyarar aikin da ya kai jihar Kebbi domin duba yadda ake gudanar da ayyukan tsaro.

Da yake jawabi ga kwamandoji da dakarun da ke kan gaba da aiki, Janar Shaibu ya buƙace su da su gudanar da ayyukan da suka dogara da sahihan bayanan leƙen asiri tare da ci-gaba da bin sawun masu garkuwa da mutane ba dare ba rana.

“Dole ne mu nemo wadannan yara. Ku dauki mataki cikin kwarewa da bin sahihan bayanai. Nasara ba zaɓi ba ce,” in ji Janar Shaibu cikin kakkausar murya.

Babban hafsan sojin ya kuma gana da masu sa kai da kuma masu farauta na cikin gari, inda ya bayyana su a matsayin muhimman abokan hulda a wannan aiki. Ya bukace su da su yi amfani da sanin da suke da shi game da dazuka da yankunan da ake zargin masu garkuwa da mutane na buya domin taimakawa sojoji wajen gano maboyarsu da kuma tarwatsa su.

“Tare za mu dawo da zaman lafiya, kuma mu tabbatar yara na komawa makaranta cikin kwanciyar hankali”, inji shi.

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Operation Fansan Yamma, Kyaftin David Adewusi ya fitar, an bayyana cewa Janar Shaibu ya kai ziyara ta jaje ga Sarkin Danko, Alhaji Abubakar Ibrahim Allaje, da kuma Shugabar makarantar GGCSS Maga, Hajiya Rabi Musa Magaji*, inda ya tabbatar musu da kudurin rundunar sojin na ganin an ceto daliban lafiya lau ba tare da wata illa ba.

Janar Shaibu ya kuma buƙaci dakarun da su ci gaba da nuna jajircewa da ƙwarewa tare da aiki da dokokin da suka shafi gudanar da ayyukan soji, a yayin da suke fuskantar kalubalen dawo da zaman lafiya a jihar Kebbi da kewayenta da ma shiyyar Arewa ta Yamma baki ɗaya.

By Babaji