Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da wani ɗalibi ɗan shekara 13 mai suna Alhassan Jamil a ƙaramar Hukumar Gwagwalada da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Alhassan ɗalibi ne a ƙaramar makarantar sakandaren Ihyau El-Burhan Academy da ke Phase 3, Gwagwalada.
Mahaifin yaron, Jamil Maikasuwa, ya ce yana kan hanyar kai ɗansa makaranta a kan babur lokacin da lamarin ya faru.
Ya bayyana cewa yayin da suke ƙoƙarin tsallake wata magudanar ruwa mai ramuka biyu, sai ya lura cewa ruwan yana gudu da ƙarfi.
A cewarsa, ya taka birki, amma ɗansa ya firgita, ya yi tsalle daga kan babur ɗin, inda ya faɗa cikin ruwan.
Maikasuwa ya ce nan take ya ajiye babur ɗin tare da ƙoƙarin ceto ɗansa, amma ruwan ya yi awon gaba da yaron.
Ya ce har zuwa ranar Laraba ba a gano gawar ɗan nasa ba.
A cewarsa, an tattaro wasu masunta da masu aikin ceto domin taimakawa wajen neman gawar yaron.
Mahaifin ya kuma ce wasu mazauna yankin da gidajensu ke kusa da bakin kogin sun bayyana cewa sun ga wata gawa a cikin ruwa, wadda ke ɗauke da jakar makaranta a bayanta.
Sai dai Maikasuwa ya bayyana fatansa na ganin an gano gawar ɗansa domin a yi masa jana’iza yadda ya kamata.
