
Daga BELLO A. BABAJI
Manyan hanyoyi da gidaje da shaguna a birnin Maiduguri, babban birnin Borno da wasu yankunan ƙaramar hukumar Jere, sun haɗe sakamakon ambaliya da ke cigaba da mamaye jihar.
Haka nan, Fadar Shehun Borno, asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da gidan zoo na Sanda Kyarimi da wasu sassan birnin na daga cikin manyan ababen al’umma da ambaliyar ta karaɗe.
Sannan, wata katangar gidan yari ta faɗi sakamakon ambaliyar wanda hakan ya sa fursunoni da dama suka tsere.
Har’ilayau, an rufe Jami’ar Maiduguri, UNIMAID da kuma Jami’ar Jihar Borno (BSU)
Kawo yanzu dubunnan mutane ne waɗanda galibin su mata ne da ƙananan yara suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar.
Baya ga mamakon ruwan sama da ake ganin shi ya sabbaba ambaliyar, akwai kuma fashewa da tafkin Alua ya yi kamar yadda rahotonni suka nuna wanda shi ma na daga cikin abin ya sa ambaliyar ta ta’azzara.
