Gwamnatin Tinubu ta lashi takobin kawo ƙarshen matsalar ambaliya a Nijeriya, inji Shettima

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ke bayyana hakan a yayin da ya yi saukar gaggawa a birnin Maiduguri inda ya kai ziyarar gani da ido kan ambaliyar da ta rutsa da dubban mutane a garin.

Mataimakin ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta sa ƙafar wando ɗaya da ƙalubalen ambaliyar ruwa a Nijeriya ta hanyar amfani da taswirar da za ta kawo maslaha ta dindindin.

Shettima, wanda ke jawabin cikin kaduwa a lokacin da yake tantance irin ɓarnar da ambaliyar ta yi a garin Maiduguri, ya jajanta wa waɗanda ibtila’in ya rutsa da su, inda ya bayyana musu cewa, shugaba Tinubu na tare da al’ummar da abin ya shafa, kuma gwamnatin tarayya za ta samar da dukkan abinda ake buƙata domin tabbatar da tsaro da tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa.

Shettima ya danganta ambaliyar da ɓallewar madatsar ruwa ta Alau wanda ya ta’azzara lamarin har ya zarce irin wanda aka taɓa samu a baya. Sai dai kuma ya jaddada aniyarsa ta samar da mafita mai ɗorewa.

Mataimakin ya kuma yi kira da a ci gaba da wayar da kan al’umma kan ƙaruwar barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa tare da jaddada aniyar gwamnati ta magance waɗannan ƙalubalen gaba ɗaya.

Shettima, ya kuma yaba wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno bisa namijin ƙoƙarin da suka nuna wajen ɗaukar matakan da suka dace akan lokaci tare da kai ɗauki ga al’ummar da lamarin ya shafa a cikin gaugawa.

By ukarofi