Ambaliyar Borno: Dabbobin daji sun tsere yayin da maƙabartu suka zagwanye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙungiyoyin al’umma (CSOs) ta ce ambaliyar da ke gudana a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya shafi aƙalla maƙabarta da wani gidan kula da dabbobin daji da kuma zagwanyewar wasu yankunan birnin.

Ƙungiyar ta nuna damuwa musamman kan al’ummar dake rayuwa a yankunan da lamarin ya shafa.

Wannan shi ne ambaliya mafi muni cikin shekaru 30 da yankin ya fuskanta tun da aka yi makamancin sa a 1994 wanda hakan ya sa mutane da dama suka rasa matsugunansu.

Cikin saƙonni ta mabanbanta hanyoyi da CSOs suka fitar, sun ce lamarin ya yi ƙamari sosai.

Shugaban CSOs na yankin Tafkin-Chad, Ahmed Shehu ya ce, kawo yanzu ba a san halin da dabbobin da suka fice daga gidan kula da su na Sanda Kyamiri suke ba.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan al’amarin.

Kazalika, Shehu ya yi kira ga ƙungiyoyin al’umma su bada agajin gaggawa musamman na abinci, kayan sakawa da kayan abinci ga waɗanda abin ya shafa.

By Babaji