
Daga BELLO A. BABAJI
Mai horar da ƴan wasan Super Eagles, Augustine Eguavoen ya ajiye aikinsa na mai jagorantar ƙungiyar.
Ya ce burinsa shi ne ya kasance a matsayin koci ga ƙungiyar na wasanni biyu kamar yadda ya bayyana a wata hira da aka yi da shi.
Eguavoen wanda shi ne Daraktan gudanarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), an naɗa shi ne bayan an gaza cimma yarjejeniyar kawo sabon koci a lokuta mabanbanta.
Ya jagoranci Super Eagles a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin Afirka da ta yi da ƙasashen Jamhuriyar Benin da Ruwanda inda ta samu jimillar mako huɗu.
