Babban hafsan tsaro ya yi wa mutanen Maiduguri jaje

Spread the love

Babban hafsan tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa a yau ya miƙa saƙon jajen sa ga mutane da da gwamnatin Maiduguri dalilin ibtila’in ambaliyar ruwa da suka tashi dashi.

Christopher Musa ya yi matuƙar kaɗuwa a dalilin labarin wannan mummunar ambaliyar da ta yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi da dama. Don haka a madadin rundunar sojojin Nijeriya ya na miƙa saƙon jaje ga dukkan al’ummar garin Maiduguri kamar yadda sanarwa ta fito daga kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Tukur Gusau.

Janar Musa ya cigaba da cewa rundunar sojojin Nijeriya za su yi aiki hannu da hannu da hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA da sauran hukumomi domin ganin an kawo ma al’ummar da abun ya shafa ɗauki cikin gaggawa. Daga nan ya umarci kwamandan Operation Haɗin Kai da ya fita su bayar da dukkan wata gudunmuwa domin kawo ɗauki.

Daga ƙarshe Janar Musa ya yi addua Allah ya jikan wanda su ka rasu, Allah ya mayar ma wanda su ka yi asara dukiya mafi alheri.

By ukarofi