Mazauna garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara sun shiga fargaba da tashin hankali sakamakon cikar wa’adin biyan harajin Naira miliyan 30 da fitaccen ɗan ta’addan nan Bello Turji ya saka musu.
Turji, wanda ya yi fice a yankin Zamfara , ya zargi mutanen garin Moriki da haɗa baki da jami’an tsaro wanda yayi sanadiyar mutuwar shanun Turjin.
Lauyan mai kare hakkin ɗan Adam Bulama Bukarti ya wallafa a shafin sa na yanar gizo irin mawuyacin halin da al’ummar garin ke ciki.
Bukarti ya ƙara da cewa, buƙatun Turjin sun haɗa da kowanne magidanci zai biya Naira 10,000 yayin da manya marasa Aure su biya Naira 2000. Wannan na nuni da cewa wannan haraji kamar diyyar dabbobin Bello Turjin ne da aka kashe.
A halin yanzu shugaban ƴan ta’addan ya na riƙe da wasu ƴan siyasa da masu fafutukar neman haƙƙin jama’a kusan 15 a yankin duk da cewa akwai sansanin soji a garin Moriki.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ƴan sandan jihar Zamfara Yazeed Abubakar ya ci tura domin har zuwa lokacin haɗa wannan labari bai amsa wayar sa ba.
Wannan lamarin dai ya cigaba da nuni da irin rashin tsaro da ke cigaba da ta’azzara a Jihar Zamfara.
