Za a samu ruwa kamar da bakin ƙwarya a jihohi 12 – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NIMET ta fitar wani hasashen za a samu ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya a jihohi 12 mako mai zuwa.

Jihohin da ake sa ran samun ruwan saman sun haɗa da Bauchi, Neja, Bayelsa, Kaduna, Plateau, Babban Birnin Tarayya (FCT), Taraba, Cross River, Akwa-Ibom, Ribas da Delta.

Sannan rahoton ya nuna cewa akwai jihohi da za a samu ruwan saman amma matsakaici, jihohin sun haɗa da Adamawa, Katsina, Zamfara, Kebbi, Nasarawa, Kwara, Benue, Ebonyi, Imo, Anambara, Edo, Ondo, Ekiti, Osun, Oyo, Ogun da Legas.

Hukumar ta NIMET ta yi gargaɗin cewa ruwan saman ka iya haifar da ambaliya musamman a kan tituna da gadoji. Hukumar daga ƙarshe ta ja hankalin mutane da su guji shiga cikin ruwa mai gudana domin gudun faɗawa cikin haɗari.

By ukarofi