Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA) ta yi kira ga al’ummar garin Faduma da ke ƙaramar hukumar Rimi da su gaggauta barin gidajensu domin kauce wa barazanar ambaliyar ruwa da ake hasashen za ta afku kafin ƙarshen watan Yuli.
Shugabar hukumar SEMA, Hajiya Binta Hussaini Dangani, ta bayyana haka a lokacin da ta kai ziyarar duba halin da al’ummar garin na Faduma suke ciki na fargabar faruwar ambaliyar ruwan zama da masu hasashen yanayi suka yi.
Ta ce “Masu hasashen yanayi sun nuna cewa akwai ƙananan hukumomi 14 a Jihar Katsina da ke cikin haɗarin ambaliya, ciki har da ƙaramar hukumar Rimi, sakamakon yiwuwar cikar dam na Are da kuma mamakon ruwan sama.
Hajiya Binta ta roƙi al’ummar Faduma su ba gwamnati cikakken haɗin kai wajen ƙaura daga yankin domin kare rayukansu da dukiyoyinsu. Ta tabbatar musu cewa gwamnatin jihar na ci gaba da duba wuraren da za a maida su cikin aminci.
A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Rimi, Hon. Muhammad Ali Rimi, ya gode wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, da hukumar SEMA da sauran hukumomin dake aiki domin kare rayuka. Ya ce ƙaramar hukumar ta tanadi wuraren da za’a mayar da mazauna garin domin gujewa haɗarin ambaliyar.
Ya ƙara da cewa majalisar zartarwar ƙaramar hukumar za ta zauna domin duba yiwuwar samar wa mazauna yankin wurin zama idan ambaliyar da ake hasashe ta faru.
Jami’in hukumar kula da noman tani ta Jihar Katsina, Engr. Abubakar Ma’azu, ya ce an gina dam ɗin tun shekarar 1980 kuma ba a taɓa yashe shi ba, yana mai bayyana cewa gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ce ta fara ɗaukar matakin yashe shi domin rage haɗarin ambaliya.
Shi ma wakilin ma’aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Katsina, Injiniya Aminu Lawal Musa, ya bayyana cewa ma’aikatarsu zata bayar da cikakken haɗin kai da tallafin da ya dace wajen kare rayukan al’umma.
Shima a nasa ɓangaren, darakta daga ma’aikatar kula da muhalli ta Jihar Katsina, Alhaji Nura Abubakar, ya ce “babu wani abin da zai iya hana ruwan shiga garin idan ya yi ambaliya”. Don haka ya jaddada cewa azo a dinga dasa itace a cikin unguwanni da rage sare itatuwa acikin unguwani da gonaki
Hukumar SEMA ta yi alƙawarin cewa nan bada jimawa ba za ta kai kayan tallafi ga al’ummar da abin ya shafa domin ƙarfafa musu gwiwa tare da kwantar masu da hankali.
