Gwamnan Jihar Borno, Babagana Uamara Zulum, ya bayyana cewa tubabbun ‘yan Boko Haram su 1,000 da suka miƙa wuya sun bar gwamnatin jihar da al’ummarta cikin wani mawuyacin halin tsaro mai baki biyu.
A cewar gwamnan, muddin gwamnati da masu faɗa a ji a jihar ba su haɗa kai sun ɗauki matakin daƙile matsalar tsaron da jihar ke fuskanta a halin yanzu ba, hakan ka iya haifar da ‘yan tawayen farar hula a jihar.
Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa shugabannin jami’an tsaro da sarakuna jawabi a Bama da Gwoza.
Ya ci gaba da cewa, matsalar tsaro a yau na buƙatar a yi mata taron dangi tsakanin masu faɗa a ji da jami’an tsaro kai, har ma da wakilan ƙananan hukumomi 27 na jihar da lamarin ya shafa, domin iya kawar da ita.
Haka nan, ya ce matsalolin sun yi ƙamarin da akwai buƙatar a dube su ta kowane ɓangare haɗa da illar da ke tattare da tubabbun ‘yan ta’addar. Yana mai cewa, wannan zai bai wa masu ruwa da tsaki damar yin ittifaki kan tsarin da ya fi dacewa a yi amfani da shi wajen cim ma muradi.
Ya ce jama’ar yankin na cikin wani mawuyacin hali dangane da ci gaba da tubar da ‘yan Boko Haram ke yi a yankin.
Gwamnan ya ce zaɓi na ga jama’a kan su zaɓi yaƙi mara ƙarewa ko kuma su amince da tubar ‘yan ta’addar wanda hakan mawuyacin al’amari ne ga duk wani da ya rasa ‘yan’uwansa sakamakon ta’addancin ‘yan ta’addan.
“Abu ne mai wahalar gaske mutum ya aminta da wanda ya kashe masa ‘yan’uwa da iyaye da ‘ya’ya. Sama da shekaru goma muna fama da wannan yaƙi, mun rasa jama’a da yawa,
“Ba mu ma san inda dubbannin ‘yan’uwanmu suke ba, ba mu ma sani ba shin suna raye ko sun mutu,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa duba da irin ɓarnar da kuma mawuyacin halin da ‘yan Boko Haram suka jefa jama’a a ciki, aminta da Boko Haram su dawo cikin al’umma na da matuƙar haɗari saboda hakan ka iya cutar da waɗanda suka cutu da Boko Haram har ya kai su ga zama ‘yan tawaye.
Kazalika, Zulum ya ce lamarin na da haɗari idan mayaƙan suka shirya yin tuba da miƙa wuya sanna kuma al’ummarsu su ƙi yarda da su.