Aminu Gwarzo ya zama ɗan takarar gwamnan Kano a NDC yayin da Gawuna ya karɓi tikitin na sanata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An zaɓi tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin tutar jam’iyyar NDC bayan da abokin hamayyarsa, Nasiru Yusuf Gawuna ya karɓi tayin jam’iyyar na tsaya wa takarar kujerar sanata a zaɓen 2027 da ke tafe.

Mai taimaka wa Gawuna na musamman, Tahir Ahmad ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa tsohon mataimakin gwamnan ya amince da tsaya wa takarar sanatan mazaɓar Kano ta Tsakiya a NDC.

Hakan na nufin kawo ƙarshen makonni ana tattaunawa acikin tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso akan sulhun tsayar da ɗan takarar gwamna.

Majiyoyi sun ce Kwankwaso ya fifita Gwarzo akan a takarar Gawuna, inda ya nemi Gawuna da gurbin mataimakin gwamna ko na sanata.

An ruwaito cewa, Gawuna ya karɓi tikitin tsaya wa sanatan ne domin ba wa Gwarzo damar zama ɗan takarar gwamnan jam’iyyar.

By Babaji