Amurka mai satar mai daga Ƙasar Sham

Daga MINA

Abokai, kwanan baya an bankado wasu ayarin motocin dakon mai na sojin Amurka sunafitar da man da suka sata daga ƙasar Sham zuwa sansaninsu dake Iraƙi ta wata hanya da ta hada ƙasar Sham da Iraƙi.

Tun daga shekarar 2015, Amurka ta fara aikata irin wannan laifi,awatan Agustan da muke ciki kaɗai, Amurka ta aikata irin wannan abin kunya na satar mai da fitar da shi zuwa Iraƙi har a ƙalla sau 6.

Yayin da fararen hula a birnin Damascus babban birnin ƙasar, ke dogayen layi don sayen man. “Duniya a zanen MINA” na zana wani hoto game da yadda Amurka ta saci mai a ƙasar Sham.

Hukumar man fetur da albarkatun ma’addinai ta ƙasar Sham ta ba da sanarwa a kwanan baya cewa, a watanni shida na farkon wannan shekara, a ko wace rana ana samar da man da ya kai ganguna dubu 80.3 a ƙasar, amma Amurka da dakarunta sun sace kaso 80% daga cikinsu.

Rahotanni na cewa, ƙasar Sham ta yi asarar kuɗaɗen da suka kai kimanin dalar Amurka biliyan 100 sakamakon satar mai da Amurka ta yi. Amma, Amurka ta nuna ko-in-kula game da sanarwar da ƙasar ta sha bayarwa.

Saboda muhimmancin man fetur din, tana yunkuri ƙwace shi, ba tare da yin la’akari da halin da al’ummar ƙasar Sham ke ciki ba ko kaɗan.

Da ma yake-yake na addabar al’ummar Sham, ga shi kuma satar man da Amurka ta yi ya yi sanadin gurgunta tattalin arziki da haifar da hauhawar farashin mai a ƙasar, abin da ya jefa al’ummar ƙasar cikin hali mai wuya.

Amurka, tana farin ciki ne da samun mai ba tare da biya ba, sai dai wa zai kwantar da hankalin jama’ar ƙasar?

Mai zane: MINA