2023: Matasan Katagum sun goyi bayan shugabancin Tinubu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Matasa a Masarautar Katagum ƙarƙashin tutar ƙungiyar ‘Katagum Youths Salvation Forum’ a Jihar Bauchi ta nuna goyon bayanta wa ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda suka bayyana a matsayin mafi dacewar ɗan takara a zaɓen shekara ta 2023.

Sun bayyana cewar, idan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar tarayyar Nijeriya, tsohon gwamnan na Lagos zai ceto ƙasar nan daga gurɓacewar tattalin arziki da take ciki a halin yanzu, ya kawar da talauchi, inganta tsarin kiwon lafiya, da daƙushe hauma-haumar siyasa, haɗi da tunɓuke cin hanci da rashawa da ya yi wa ƙasar nan katutu.

Shugaban ƙungiyar, Kwamared Umar Idris Chinade ya bayyana cewar, sun bijiro da tsare-tsare na wayar da kan jama’a, musamman masu jefa ƙuri’a dangane da wanda za su zaɓa a shugabanci idan zaɓen shekarar 2023 ya gabato.

Umar Chinade ya shaida wa manema labarai a garin Azare, shalkwatar ƙaramar hukumar Katagum a kwanakin baya cewar, matuƙar an samu wayewar kan jama’a da nusar da su kan wajiban siyasar ƙasar Katagum da Nijeriya baki ɗaya, zaɓen shekara ta 2023 zai tabbatar da samun jajirtattun shugabanni da zasu yi fatali da gurɓatattu waɗanda suka lalata tattalin arzikin ƙasar nan, tare da sakacin yawaitar ƙalubalolin tsaro da suka buwayi ƙasa.

Chinade ya kuma lura da cewar, tsohon gwamnan na jihar Legas wanda hamshaqin attajiri ne, ba zai saci kuɗaɗen hukuma ba, ko ya jirkita tattalin arzikin ƙasar ya zuwa son zuciya, maimakon ma haka, zai bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya ne, samar da romon dimukuraɗiyya da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, haɗi da rage kaifin talauci a tsakanin al’ummar ƙasa.

“A halin yanzu, ƙungiyar mu tana gudanar da tarurruka ne a zaurukan jama’a a mazaɓu daban-daban dake yankunan masarautun Katagum da Jama’are waɗanda suke da ƙananan hukumomi guda bakwai, sune Katagum, Jama’are, Zaki, Gamawa, Giade, Shira, da Itas/Gadau, domin faɗakar da jama’a akan illolin zaɓen shugabannin jeka-na-yika.

Comrade Umar Chinade ya kuma bayyana cewar, ƙungiyar tasu tana da wasu ƙananan ƙungiyoyi masu rajista kimanin guda hamsin waɗanda suke barbaje a matakan ƙananan hukumomi, hakimai, Dagatai da masu unguwanni a cikin masarautun guda biyu, kan ire-iren shugabanni da ya kamata su zaɓa a zaɓen gamagari na baɗi.