An yaba wa ɗan sandan Nijeriya da ya ƙi karɓar cin hancin sama da Naira miliyan 83

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ya yaba wa wani ɗan sandan ƙasar da ya ƙi karɓar cin hancin dala 200,000 kwatankwacin Naira miliyan 83.87.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ƙasar ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Laraba, an kuma yaba wa wasu ‘yan sanda biyu bisa jajircewarsu bisa ayyukansu.

Sanarwar, wadda kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya sanya wa hannu, ta ambato babban sufeton ‘yan sandan yana bayar da umarni a bai wa ‘yan sandan uku takaradar shaidar nuna ƙwazo bisa ayyukansu duk kuwa da ƙalubalen da suke fuskanta.

“Ɗaya daga cikin ‘yan sandan shi ne SP Daniel Itse Amah, DPO na Nasarawa da ke Jihar Kano, wanda aka yaba masa bisa tsare gaskiya da iya gudanar da aiki abin da ya kai shi ga kama wani gungun ‘yan fashi da makami da suka ba shi cin hancin dala 200,000 amma ya ƙi amincewa,” inji sanarwar.