An kama wani ɗalibi ɗan shekara 18 bisa yunƙurin yin garkuwa da shugaban makaranta a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an Hukumar Tsaron Al’umma ta Nijeriya (NSCDC), reshen Jihar Neja sun kama wani ɗalibi ɗan shekara 18 da haihuwa, bisa zargin yunƙurin yin garkuwa da Shugaban Makarantar Koyon Noman Kifi a Sabuwar Bussa.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASC Nasir Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba.

Ya ce wanda ake zargin, wanda ɗalibin kwalejin ne, ya haɗa baki da wani mutum ɗaya, wanda a halin yanzu, ya rubuta wasiƙar barazanar yin garkuwa da Provost idan ya kasa biyan kuɗin fansa.

Sai dai Nasir ya ce wanda ake zargin bai buƙaci wani adadi na musamman ba kafin jami’an tsaro su kama shi.

Kakakin ya ƙara da cewa, nan take aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata babbar kotun majistare kan laifuka biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma razanarwa.