‘Yan sanda sun samu nasarar hallaka varayin daji masu tarin yawa a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar katsina ta ce jami’anta sun hallaka ‘yan ta’adda da kawo yanzu ba a tantance yawansu ba a yayin wani gumurzu da ya haddasa musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar lamarin dai ya faru a yankin Ƙaramar Hukumar Kurfi.

A yayin artabun rundunar ta samu nasarar ƙwato tumaki 72 da awaki 34 gami da shanu 2 daga hannun ‘yan ta’addar.

Musayar wutar dai ta faru ne a ƙauyukan Dadawa da Barkiya na karamar hukumar, kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana.

SP Isah ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa dake nuni da cewar wasu ‘yan ta’adda ɗauke da muggan makamai da yawan su ya kai kimanin 80 a kan babura sun kai hari a ƙauyukan Dadawa da kuma Barkiya.

Ya ci gaba da cewa samun kiran ke da wuya sai rundunar ta tura jami’anta na musamman waɗanda suka tunkari ‘yan bindigar suka kuma shiga musayar wuta da su, inda suka kashe wasu tare da raunata wasu da dama.

Kakakin rundunar ya kuma bayyana cewar jami’an ‘yan sanda na ci gaba da bincike a yankin da lamarin ya faru don kamo sauran ‘yan ta’addar da aka raunata.

A nashi ɓangaren kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Idris Dauda Dabban ya yaba da ƙwazon jami’an na sa ya kuma roƙi al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa rundunar goyon baya don samun nasarar kakkaɓe ‘yan ta’addar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *