Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin binciken zargin karkatar da Naira miliyan 352 a Jami’ar Wudil

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamitin da zai binciki zargin karkatar da Naira miliyan 352 a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil a jihar.

A kwanakin baya ne wani kwamiti da aka kafa don binciken mahukuntan jami’ar kan zarge-zarge ya miƙa rahotonsa ga gwamnati.

Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar kuma har da na buƙatar bincikar yadda ake zargin karkatar da kuɗaɗen, waɗanda aka ce na fanshon ma’aikatan jami’ar ne.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da kafa kwamitin a cikin wata sanarwa da rabawa manema labarai a ranar Talata da ta gabata.

Ya ce Gwamna Ganduje ne ya kafa kwamitin wanda ya ƙunshi hukumomin gwamnati da dama domin bin diddigin zarge-zargen.

A cewar kwamishinan, kwamitin zai kasance ƙarƙashin manyan sakatarori na Ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar da ofishin sakataren gwamnatin jihar da na asusun ’yan fansho da na ma’aikatar kuɗi da babban mai bincike na jihar.

Sauran sun haɗa mai bincike na ƙananan da shugaban huukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar da Babban Sakataren ma’aikatar Ilimi waɗanda dukkansu za su kasance mambobin kwamitin.

Bugu da ƙari, sanarwar ta ce babban sakataren ma’aikatar shari’a na jihar ne zai kasance sakataren kwamitin.

Kwamishinan ya kuma ce nan ba da jimawa ba gwamnan zai rantsar da kwamitin a wata ranar da za a sanar a nan gaba.