Za mu taimaka wajen yaɗa littattafan Sheikh Farouk Cheɗi – Sa’adatu Rimi

Daga MIUHAMMADU MUJJITABA a Kano

An bayyana cewa littattafai da sauran bayanai na na ilimi wasu a rubuce wasu ma ba a buga littattafan ba, dama kasat-kasat, na Marigayi Sheikh Yahaya Faruku Cheɗi abu ne da su ke da matuƙar muhimmanci wajen fito da ilimi a cikin su.

Don haka littattafan da aka buga su a yanzu da kuma wanda za a bugasu a nan gaba za su tsaya tsayin daka wajen ganin sun kaisu makarantar Sa`adatu Rimi da ma sauran kwalejoji ilimi na Kano da taimaka wajen yaɗa su ga al’umma domin jama’a na yanzu da masu zuwa nan gaba su amfana da gudunmawar da Sheikh Yahaya Farok Chiɗi ya bayar a lokacin rayuwarsa.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Dakta Kabiru Gwarzo, Mataimakin Shugaban Kwalejin Ilimi ta Kumbotso a lokacin taron addu’a da tunawa da Marigayi, ɗan gwagwarmaya Malam Yahaya Farok Chiɗi wanda aka yi a karo na farko ƙarƙashin shugabancin babban limamin Kano, Farfesa Sani Zahradden, wanda Farfesa Sheikh Umar Sani Fagge ya kasance babban baƙo mai jawabi, kuma ɗaya daga cikin makusanta Marigayi Sheikh Yahaya Farok Cheɗi a taron da aka yi a Makrantar Nazarin Harshen Larabci ta SAS Kano a ranar Lahadin da ta gabata.

Har illa yau Dakta Kabiru Gwarzo ya ƙara da cewa rayuwar Malam Farouk na cike da darusa masu yawa da ya koya, inda ya bayyana akwai haƙuri, jajircewa, ƙwazo da rashin gajiyawa, inda ya ce ba zai manta da wannan darusa ba, kuma zai cigaba da duk wani abu na taimakawa da sa da zumunci ga iyalai da ‘yan uwan Malam Yahaya Farouk Cheɗi.

Shi ma Malam Abubakar Na’abba shugaban cibiyar Manifold, da ta shirya taron tunawa da Malam Farouk Cheɗi ya ce yanzu haka, akawai qasa kasai guda 297 da Marigayi ya gabatar da jawabai daban-daban a kan maudu’I daban-daban na ilimi kuma ya kai shekara 40 yana ɗaukar waɗanan bayanai daga Malam Yahaya Faruku Cheɗi da abokinsa Sheikh Umar Sani Fagge, wanda shi kuma kasansa da Cibiyar Manifold ta ke da shi sun haura 1,000 wasu kuma an mayar da su littattafai don amfanin al’umma wanda yanzu haka a cewarsa suna ƙoƙarin zamanartar da su da yaɗa su ta kafofin sadarwa na zamani, jarida da rediyo, gwargwardon gudunmawa da haɗin kan al’umma a wannan aiki na alkairi.

A ƙarshe Farfesa Sheikh Umar Sani Fagge da shugaban majalisar malamai na Arewa Sheikh Ibrahim Khalil sun bayyana muhimmancin wannan taro da kuma cigaba da shi domin taimakawa ga iyalan irin waɗannan malamai da suka bada gudunmawa ta ilimi a rayuwarsu dukkaninsu su bayyana Malam Yahaya a matsayin malami jarimi da ya fifita ilimi da koyarwa fiye da komai a rayuwarsa, musamam kasancewarsa babban kwamandan hukumar Hisba na farko wanda kuma shi ya rubuta kundin Hisba da ake amfani da shi yanzu haka a Kano.