Matasa sun nutse a ruwa a yayin da suke murnar cin jarrabawa a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Legas ta ce wasu matasa huɗu sun nutse a ruwa a yayin da suke murnar cin jarrabawar kammala sakandire.

Lamarin ya afku ne a ranar Talata a tekun Elegushi da ke unguwar masu galihu ta Lekki.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa matasan sun nitse bayan sun karvi sakamakon jarrabawarsu daga makaranta.

Hukumar gudanarwar tekun ta ce mamatan na daga ckin ɗalibai 10 da suka je wajen don yin murnar samun nasara a jarrabawarsu ta kammala karatun sakandire.

Mai magana da yawun hukumar gudanarwar ya ce yaran sun bijirewa gargaɗin da jami’an da ke kula da tekun suka yi musu.

Kawo yanzu dai mahukunta ba su bayyana shekarun yaran ba ko kuma daga in da suka fito ba.

Jihar Legas dai na kewaye da ruwa da kuma wuraren shaƙatawa abin da ya sa mutane kan je don shaƙatawa ko kuma gudanar da wani biki a bakin teku.