Amurka mai son ƙaƙaba takunkumi ta kawo babbar illa ga duk faɗin duniya

Daga AMINU XU

Abokai na, yau “Duniya a zanen MINA” na mai da hankali kan Amurka mai matuƙar son ƙaƙaba takunkumi ga saura. Rahoton da ma’aikatar kuɗin Amurka ta bayar mai taken “Kimanta takunkumin da Amurka ta sanyawa sauran ƙasashe a shekarar 2021” na nuna cewa, shekaru 20 da suka gabata, tun ɓarkewar rikicin “9.11”, yawan takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa sauran ƙasashe ya karu matuka. An ce, ya zuwa ƙarshen shekarar 2021, yawan takunkumin da Amurka ta ƙaƙƙaba wa sauran ƙasashe ya kai fiye da 9400, inda yawansa ya ninka sau 10 bisa na shekaru 20 da suka gabata.

Irin wannan takunkumi tamkar matsin lamba ne ga wasu ƙasashe marasa ƙarfi, abin da ya haifar da koma bayan tattalin arziki da zaman takewar al’ummarsu. Jaridar “USA TODAY” ta yi hasashen cewa, bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan, yawan fararen hula da suka mutu sakamakon takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasar, ya fi na waɗanda suka rasu a cikin yaki na tsawo shekaru 20. Ban da wannan kuma, takunkumin da Amurka ta sanyawa ƙasashen Iran da Venezuela da sauran ƙasashe masu arzikin man fetur, ya hana su fitar da man fetur zuwa ƙetare, matakin da ya sa suka fama da koma bayan tattalin arziki.

Amma shin Amurka ta cimma burinta ta yin amfani da makamin sanya takunkumi? A’a, a haƙiƙa wasu kafofin yaɗa labarai a duniya da manazarta sun yi nuni da cewa, amfani da takunkumin da Amurka take sanyawa ya bayyana raguwar ƙarfinta a duniya.

Ƙaƙaba wa sauran ƙasashe takunkumi a matsayin wata ƙasa mafi girma, don tilasta musu durƙusawa gabanta mataki ne da ba za a yarda da shi ba, kuma ya kamata ƙasashe daban-daban sun kara fahimtar juna da cin moriya tare. Ya kamata Amurka ta fahimci wannan ba tare da bata lokaci ba, don tabbatar da zaman lafiya da ƙarko a duniya tun da wuri. Idan wata ƙasa ta nuna karfin tuwo, ko sanya takunkumi yadda take so don biyan moriyar ƙashin kanta kawai, to ba bu shakka za a mayar da martani bisa iyakacin ƙoƙarinsa. Game da wannan batu, ga Cartoon da na zana.

Mai zane: Amina Xu