Ƙasashen Afirka na ƙara amfana daga alaƙarsu da ƙasar Sin

Daga IBRAHIM YAYA

Tun bayan da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya yi bayani game da manufar ƙasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar ƙasashen Sin da Afrika a sabon zamani, wadda yanzu haka ta haifar da ƙawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin ɓangarorin biyu.

Ita dai wannan manufa da shugaba Xi Jinping ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban ƙasar Sin, a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna.

Bisa waɗannan tsare-tsare, ƙasar Sin da Afrika, sun hada ƙarfi da ƙarfe, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai ɗaya, da nufin samar da dangantaka mai ƙarfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin ƙasar dake nahiyar Asia da kuma nahiyar Afrika, waɗanda yawan al’ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin ɗaya bisa ukun al’ummar duniya baki ɗaya.

Bayan waɗannan shekaru, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin ƙasar Sin da nahiyar Afrika a fannoni da suka hada da tattalin arziki, da ilimi, da cinikayya, da kayayyakin more rayuwa, da al’adu, da fannin aikin gona, da raya masana’antu da ma kai wa juna ziyara a bangaren manyan jami’ai da shugabannin sassan biyu.

Tarukan dandalin hadin gwiwar ƙasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, da suka gudana a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Beijing na ƙasar Sin da na baya-bayan nan a Dakar na ƙasar Senegal, gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin ɓangarorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al’ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare.

Sai dai duk da irin wannann ci gaba da sassan biyu suka samu, ƙasashen yamma sun sha yiwa wannan alaƙa wata mummunan mahuguwar fahimta, har ma suka nemi bata wannan dangantaka ta fannoni daban-daban. Sai dai bakin alƙalami ya riga ya bushe, kuma hakar su ba za ta taba cimma ruwa ba.

Sakamakon wannan haɗin gwiwa, ƙasashen Afrika da Sin, suna ƙoƙarin haɗe manufofi da dabarunsu na samun ci gaba ƙarƙashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da muradun ci gaba masu ɗorewa na MDD da kuma ajandar raya nahiyar ta ƙungiyar Tarayyar Afrika da ake son cimmawa nan zuwa shekarar 2063. Alaƙar sassan biyu, tana ƙara taka muhimmiyar rawa a fannonin inganta rayuwar bil-Adam, matakin da masana suka yaba matuƙa.

Abubuwa na baya-bayan nan da wasu ƙasashen Afirka suka amfana da shi daga alaƙarsu da kasar Sin su ne, ƙaddamar da babbar gadar Foundiougne mai tsawon mita 1600 da kamfanin ƙasar Sin ya gina ta hanyar rancen kuɗin da ƙasar ta nema daga ƙasar Sin. Aikin dake zama daya daga cikin manyan ayyukan da ake gudanarwa bisa “shirin farfaɗo da Senegal”, kana ayyukan haɗin gwiwa goma ƙarƙashin huldar Sin da ƙasashen Afirka. Sai kuma ginin wata hanya mai tsaown kilomita 100 dake tsakiyar Kumasi, birni mafi girma na biyu a ƙasar Ghana da sauransu.

Masana na ganin cewa, irin waɗannan ayyuka za su inganta da ma sauƙaƙa harkokin zirga-zirga, baya ga ƙara samar da kuɗaɗen shiga, matakin da zai kara inganta rayuwar mazauna wuraren. Sin da ƙasashen Afirka na kara zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.