Ma’aikatar Wajen Ƙasar Sin ta mayar da martani game da ɓarkewar tashin hankali a wasu sassan Sudan ta Kudu

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, Larabar nan ya shirya taron manema labarai na yau da kullum. Kuma wani dan jarida ya yi masa tambaya cewa, a baya-bayan nan an samu tashe-tashen hankula a wasu sassan Sudan ta Kudu. Shin mene ne ra’ayin ƙasar Sin?

Wang Wenbin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu, an samu gagarumin ci gaba a yunƙurin samar da zaman lafiya a ƙasar Sudan ta Kudu, wanda kuma ya dace da muhimman muradun al’ummar ƙasar. Ƙasar Sin tana kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, da su mutunta nasarorin da aka samu na zaman lafiya, da ci gaba da warware sabanin ra’ayi ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Yayin da yake ƙarin haske kan rikicin dake faruwa tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine kuwa, Wang Wenbin ya bayyana cewa, ƙasar Sin tana goyon baya tare da karfafa dukkan matakai na diflomasiyya, da za su taimaka wajen warware rikicin ƙasar Ukraine cikin lumana.

Haka kuma, Wang Wenbin ya ce, a ko da yaushe gwamnatin ƙasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa jagorancin ƙungiyar cinikayya ta duniya.

Mai fassarawa: Ibrahim