Za a gudanar da taron ƙolin Sin da EU ta kafar bidiyo a ranar 1 ga Afrilu

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya sanar yau Laraba cewa, za a gudanar da taron ƙoli na Sin da EU karo na 23 ta kafar bidiyo a ranar Juma’a.

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da kuma firaministan ƙasar Li Keqiang, za su gana da shugaban majalisar gudanarwar ƙungiyar Tarayyar Turai Charles Michel da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar, uwar gida Ursula von der Leyen yayin taron.

Mai fassarawa: Ibrahim