Daga BASHIR ISAH
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da a haɗe kai wuri guda sannan a yaƙi ‘yan ta’adda da ta’addancinsu a faɗin ƙasa.
Sanata Adamu ya yi wannan kira ne biyo bayan mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da ta gabata.
Cikin sanarwar da ya fitar a jiya Laraba, Shugaban APCn ya ce lokaci ya yi da ya kamata ‘yan ƙasa su haɗa kai wajen yaƙar maƙiyan ƙasa.
Daga nan, ya nuna alhininsa dangane da rashe-rashen da kuma raunukan da aka samu yayin harin tare da miƙa ta’aziyyarsa ga ahalin marigayan.
A cewar Sanata Adamu, “Na yi Alla-wadai da wannan harin. Lamarin ya munana, kuma harin ya nuna yadda maƙiya za su yi dukkan mai yiwuwa wajen lalata ƙoƙarin da gwamanati ke yi wajen tabbatar da Nijeriya a matsayin ƙasa mai cikakken tsaro.
“Ina kira ga ‘yan Nijeriya su kalli wannan hari a matsayin aikin ‘yan ta’adda, maɓarnata waɗanda ba su ƙaunar zaman lafiyar ƙasar nan.
“Dole ne mu dunƙule mu yaƙi waɗanda ke lalata cigaban ƙasa da kuma dimukraɗiyyarmu.”