Amurka ta gurfanar da Nicolás Maduro da matarsa kan makircin cin zarafi da wasu laifuka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Amurka ta sanar da gurfanar da tsohon Shugaban ƙasar Venezuela Nicolás Maduro da matarsa, Cilia Flores bisa zargin su da hannu a makircin aikata cin zarafi, wanda ke nuna an samu ƙarin sabon zargin aikata babban laifi ga tuhume-tuhumen safarar ƙwayoyi da suke fuskanta.

A bayanan da aka fitar a birnin New York daga baya a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2026, ana zargin Maduro da Flores da umarta da sanya ido akan wani salon cin zarafi, tserewa ba bisa doka ba da rikici akan abokan hamayyar siyasa yayin shekaru 13 na mulkinsu.

Haka kuma, an zargi mutanen biyu da neman su cigaba da jagoranci ta hanyar cin zarafi da gurfanar da ‘yna ɓangaren adawa, wanda hakan ya sa aka tozarta dubunnan ‘yan ƙasar, yi musu barazana da kama su. Akwai kuma gurfanarwa, cin zarafi, duka ko halaka dukkan waɗanda suke adawa da gwamnatin.

Zarge-zargen sun kuma haɗa da amfani da wasu ababe wajen cutar da ‘yan ƙasa, ciki har da lantarki, duka da ɗimautarwa. Hallau, tuhume-tuhumen ya haɗa da zargin Maduro da barazanar halaka ɗan wani fursuna a matsayin horo a gare shi.

Wannan sabon zargin ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi wa Maduro da matar tasa ne na tuhumar su da kitsa makircin safarar hodar ibilis zuwa cikin ƙasar Amurka.

A ranar 3 ga Junairu ne jami’an sojin Amurka suka kama Mauro da Flores a gidansu da ke yankin Caracas, sannan suka gurfanar da su a wata kotun New York bisa zargin su da hannu a lamuran ƙwayoyi. Saidai sun musanta cewa ba su da hannu a abin da ake tuhumar su a kai, inda daga lokacin ne aka tsare su a gidan yari na Metropolitan Detention Centre da ke Brooklyn. Za a fara shari’arsu a ranar 1 ga Yuni, 2027.

By Babaji

Leave a Reply