
Amurka na shirin janye sojojinta kusan guda 5,000 daga Jamus, a daidai lokacin da taƙaddama ke ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu akan batun yaƙin Iran, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Shugaba Donald Trump ya zargi ƙawayen Turai da rashin nuna cikakken goyon baya ga yaƙin, lamarin da ya janyo rashin jituwar difulomasiyya a tsakaninsu.
A nasa ɓangaren, Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya zargi Amurka da fuskantar ƙasƙanci daga Iran yayin da ake tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin.
Rahoton ya ce, ana sa ran janyewar sojojin za ta gudana ne cikin watanni shida zuwa goma sha biyu masu zuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Pentagon ne ta yanke wannan shawara a ranar Juma’a, kwanaki kaɗan bayan furucin da shugaban gwamnatin Jamus ya yi dangane da halin da ake ciki a tattaunawar zaman lafiya.
