Daga AISHA ASAS
An kafa dokar ta-ɓaci a yankin Kursk na ƙasar Rasha yayin da ake ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan iyakokin ƙasar da dakarun Ukraine su ke yi.
A cewar BBC, gwamnan riƙon ƙwarya na yankin Aleɗei Smirnoɓ, ya ce, matakin ya zama dole “domin kawar da tasirin harin da sojojin maƙiya ke yi a yankin.”
Jami’an Rasha sun ce, aƙalla fararen hula biyar ne suka mutu, yayin da 31 suka jikkata, shida daga cikinsu ƙananan yara ne.
A ɓangaren abokiyar yaƙin nata, wato Ukraine, har zuwa yanzu ba ta ce komai ba a hukumance kuma har yanzu ba a san zurfin kutsen ba.
Moscow ta ce, a safiyar Talatar da ta gabata, sojojin Ukraine kusan 1,000, da tankokin yaƙi 11 da motocin yaƙi sama da 20, sun shiga ƙasar Rasha kusa da garin Sudzha.
Rahotanni sun ce, an gwabza faɗa ne a ƙauyuka da dama a duk ranar Talatar, inda hukumomin yankin suka buƙaci mazauna yankin da su takaita zirga-zirga, kuma an soke duk wani taron jama’a.
An gudanar da zagayen gargaɗi da dama a Kursk, wanda wani faifan da aka buga ta intanat, wanda BBC ta tabbatar, ya nuna jiragen yaƙi na ta shawagi a ƙasa, inda hayaƙi ke tashi daga yankunan da ke ƙasar.
An kwashe dubunnan mutane daga yankunan kan iyaka, kuma an shigo da likitoci daga wasu garuruwa, inji Mista Smirnov.
