An samu tagomashi a ɓangaren lantarki – Minista Adelabu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya ya samar da megawatts na wutan lantarki a ranar 27 ga watan Yulin 2024, inda ya bayyana shi a matsayin tsawon shekaru uku.

Adelabu ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙaddamar da cibiyar samar da wutar lantarki ta ma’aikatu a Abuja ranar Laraba.

Yayin da yake bayyana nasarorin da aka cimma da kuma manufofin da za a cimma a nan gaba a fannin wutar lantarki, Ministan ya ce, “A ’yan kwanakin da suka gabata, a ranar 27 ga watan Yuli, mun samu nasarar samar da wutar lantarki mai ƙarfin 5,105MW, wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru uku da suka gabata. Wannan ci gaba ne daga ƙarfin da ya gabata na kusan 4,000MW ko ƙasa da haka.

“Manufarmu ita ce cimma wani muhimmin tsari na samar da 6,000MW nan da Disamba.”

Domin amfani da ƙarfin tattalin arzikin ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya, ministocin gwamnati a taron sun yi kira da a ƙara haɗin gwiwa a ma’aikatu da sassa daban-daban.

Sun jaddada muhimmiyar rawar da ɓangaren ke takawa wajen bunƙasa tattalin arziki da masana’antu, tare da daidaitawa da hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu.

Adelabu ya jaddada wajabcin haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatun domin cimma waɗannan manufofin.

By ukarofi