Har yanzu matatun man gida ba su samun ɗanyen mai a Naira ba – CORAN

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

ƙungiyar Masu Mallakin Matatar ɗanyen Mai ta Nijeriya, CORAN, ta bayyana cewa har yanzu mambobinta ba su fara sayen ɗanyen mai a Naira ba, duk da amincewar da Gwamnatin Tarayya ta yi a baya-bayan nan.

Sakatariyar hulɗa da jama’a ta CORAN, Echie Idoko, ta bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na Channels, inda ta bayyana buƙatar samar da ƙa’idoji don aiwatar da umarnin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC).

Majalisar ta amince da sayar da ɗanyen man fetur ga matatun man Nijeriya da suka haɗa da matatar Dangote a naira domin sauƙaƙa shiga da kuma rage matsin canjin kuɗaɗen waje. Duk da haka, ba a aiwayar da manufar ba saboda rashin ƙayyadaddun ƙa’idoki da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki.

Idoko ya jaddada cewa ba tare da takamaiman ƙa’idoji daga hukumomin da suka dace ba, ba za a iya aiwatar da umarnin yadda ya kamata ba.

Ya bayyana fatan cewa gwamnati za ta haɗa da masu ruwa da tsaki a masana’antu don kafa tsarin da zai iya aiki.

A cewarsa, dole ne a samar da ƙa’idoji daga hukumomin da suka dace da za su yi bayanin yadda ake samun ɗanyen man a Naira.

“Mun ambaci wajen da muke ta fuskoki da dama. Kamar yadda yake a yanzu, babu ɗaya daga cikin membobinmu da ya fara tada ɗanyen mai a Naira. Tabbas, mun ambaci cewa furcin yana maraba, amma har yanzu akwai ’yan matakai da ya kamata a ɗauka don aiwatar da shi. Sanarwar majalisar zartarwa ta tarayya ce kawai. Akwai buƙatar samar da tsarin da zai ba mu damar samun ɗanyen mai a Naira.

“Dole ne a samar da jagora kan yadda za mu iya shiga. Dole ne mu san ainihin adadin da ke zuwa mana a Naira. Duk waɗannan bayanan dole ne a yi aiki da su. Mun san shela ce ta kwanan nan, don haka za mu baiwa gwamnati shakku.

By ukarofi