An binne wata tsohuwa cikin akwatin gawa mai siffar kwalbar Coca-Cola a Bayelsa

Spread the love

An gudanar da wani gagarumin jana’iza a ƙauyen Emeyal 1 na ƙaramar Hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, inda aka binne wata tsohuwa mai suna Madam Afuwari Ego, wadda aka fi sani da Ego Na Money, cikin akwatin gawa mai siffar kwalbar Coca-Cola, abin da ya ɗauki hankalin al’umma.

An gabatar da jana’izar ne a ranar Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, kuma tun daga buɗe shi mazauna yankin suka taru suna kallon wannan salo mai ban mamaki da bai saba faruwa ba. 

Hotunan da Ogbara Walson Henry ya wallafa sun nuna yadda aka ƙera akwatin da fasaha, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce da yabo a wajen taron.

Masu halarta sun bayyana jana’izar a matsayin wadda ta kasance ta musamman, suna cewa wannan salon ya dace da halayen marigayiyar da ta kasance cike da nishaɗi da walwala.

Dalilin iyalanta na zabar kwalbar Coca-Cola:

Iyalan marigayiyar sun bayyana cewa sun yi wannan ra’ayi ne domin girmama ƙaunarta ta musamman ga Coca-Cola, abin sha da ta shafe rayuwarta tana matuƙar so.

Marigayiya ta rasu tana da shekara 85, ta bar tarihi da kuma jana’izar da mutane za su daɗe suna tunawa da ita saboda salo da ƙirƙirar da aka yi wajen binne ta.

By ukarofi