Rahotanni sun bayyana cewa an tuntuɓi David Beckham, domin ya goyi bayan sayar da Manchester United.
A raɗe-raɗin da ake yi wasu attajirai masu zuba hannun jari daga Haɗaɗɗiyar Daulal Larabawa ne ke shirye-shiryen sayen hannun jarin da iyalan Glazer suka mallaka.
Kamar yadda Star da Mirror ta wallafa, attajiran na son Beckham ya zama jakada a lokacin da za a yi cinikin.
Tsohon ɗan wasan United, wanda yake da hannun jari Inter Miami da Salford, zai iya samun damar mallakar hannun jari a ƙungiyar Old Trafford.
Beckham wanda ya daɗe yana caccakar iyalan Glazer kan yadda suke gunadar da United ya taɓa buƙatar su sayar da ƙungiyar a 2023, ya kuma ce a shirye yake a dama da shi nan gaba a gudanar da ita.
Sir Jim Ratcliffe mai kamfanin Ineos Group ne ya mallaki haƙƙin tafiyar da United, bayan da ya mallaki hannun jarin kaso 27.7 a Fabrairun 2024.
A cikin watan Mayu ne aka sanar da niyyar mahukuntan United kan gina sabon filin wasan da zai ci ’yan kallo 100,000 kusa da Old Trafford, sai dai ƙungiyar ba ta ƙoƙari a wasannin da take bugawa.
