Kano Pillars ta dakatar da mai horar da ’yan wasanta

Spread the love

Hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da masu horas da ƙungiyar bisa jagorancin Ogenyi Evans da mataimakinsa Ahmed Yaro Yaro.

Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyar ta sha kashi a hannun Barau FC a karawar da suka yi ranar Lahadi a gasar Premier ta Nijeriya.

Sanarwar da hukumar gudanarwar ƙungiyar ta fitar ta ce an dakatar da kocin da mataimakinsa ne “sanadiyyar rashin ƙowari a gasar Premier ta Nijeriya ta 20025/26 da ke gudana.”

Ya zuwa yanzu Pillars ta yi nasara a wasanni biyu ne kacal cikin wasa takwas da ta buga a wannan kaka, inda ta yi rashin nasara a wasa huɗu sannan ta yi canjaras a biyu.

Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta ce a yanzu an naɗa tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar Gambo Muhammad da mai horas da mai tsaron gida Sulaiman Shuaibu a matsayin waɗanda za su ja ragamar ƙungiyar na wucin-gadi.

By ukarofi