An buƙaci gwamnati ta tallafa wa fannin kiɗa don bunƙasa tattalin arziki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An buƙaci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta ƙara zuba jari a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha irin na kaɗe-kaɗe, domin ta iya bunƙasa tattalin arzikin ƙasar tare da samar da damar haɓaka baiwar matasa da suke tasowa.

Daraktan Kiɗa na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), Kyaftin na Runduna Oludare Ayanbode, ne ya yi wannan kira yayin da yake ɗaya daga cikin alƙalan da suka jagoranci gasar kiɗa ta ƙasa a Abuja karo na takwas, wato Abuja National Music Competition (ANMC).

A cewarsa, har yanzu akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen gano baiwar yara tun suna ƙanana tare da ƙarfafa sha’awarsu ga harkar kiɗa da sauran fannoni na fasaha.

Shi ma Babban Jami’in Gudanarwa na Makarantar Kiɗa ta Abba Music School, kuma ɗaya daga cikin masu shirya gasar, Dakta Nana Gbolahan, ya bayyana cewa babban dalilin gudanar da gasar shi ne bunƙasa al’adun kiɗa da ilimin kiɗa musamman a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Gasar ANMC wata gasa ce da aka tsara domin ɗaliban makarantun firamare da sakandare a Abuja, da nufin ƙarfafa koyar da kiɗa tare da bai wa matasa damar nuna baiwarsu.

An kuma tsara gasar ne domin gano hazaƙa, ƙarfafa tarbiyya ta hanyar fasaha da kuma haifar da tattaunawa kan muhimmancin kiɗa a tsarin ilimin Nijeriya.

Ayanbode ya ce gasar bana ta bai wa makarantu da dama damar shiga, lamarin da ke nuna cewa makarantu na ƙara bai wa koyar da kiɗa muhimmanci.

“Wannan ya nuna cewa makarantu da dama sun fara ƙarfafa koyar da kiɗa, kuma hakan ya taimaka wajen fito da baiwar matasa masu yawa da kuma zama abin koyi ga sauran yara,” inji shi.

Ya bayyana kiɗa a matsayin wata hanya ta ilimi da ke ƙara ƙarfin tunani da inganta ƙwaƙwalwa, yana mai cewa bai kamata a raina muhimmancinsa ba.

A cewarsa, gwamnati ta yi wasu matakai wajen tallafa wa fannin, amma har yanzu akwai sauran aiki.

“Ba zan ce gwamnati ba ta yi abin kirki ba, amma ina ganin akwai damar yin ƙarin ƙoƙari wajen gano baiwar yara tun suna ƙanana da kuma haɓaka su.

“Ya kamata a ba koyar da kiɗa kulawa sosai a makarantun firamare da sakandare. Haka kuma manhajar karatun ta kasance mai ƙarfi ba kawai a makarantu masu zaman kansu ba har ma da na gwamnati. Wannan zai taimaka wajen samar da ƙarin masu baiwa tare da taimaka musu a sauran fannoni na karatu da rayuwa,” inji shi.

A nata ɓangaren, Dakta Gbolahan ta bayyana cewa manufar gasar ita ce ƙarfafa al’adun kiɗa da kuma samar wa matasa dandamalin nuna hazaƙarsu.

“Kiɗa harshe ne na zuciya, kuma dukanmu muna cikin wannan harshe. Babban abin da ke ƙarfafa ni shi ne ci gaba da bunƙasa harkar kiɗa musamman a Abuja.

“A wasu sassan Nijeriya kamar Legas, kiɗa ya daɗe yana samun karɓuwa sosai, amma a Abuja yana ƙara samun tagomashi ne a hankali, kuma yanzu ya fi yadda yake a baya,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, yara da dama suna da baiwa ta halitta, amma ba sa samun damar da za su nuna ko bunƙasa wannan baiwa.

“Mun samar da wannan dandali ne domin su iya fafatawa, su haɗu da sauran yara masu irin wannan sha’awa, tare da samun damar ƙara haɓaka basirarsu,” ta bayyana.

Masu ruwa da tsaki a fannin sun yi amannar cewa ƙarin saka hannun jari a harkar fasaha da kiɗa zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki da kuma ba wa matasa damar amfani da baiwarsu wajen gina makomarsu.

By ukarofi